Sunday, November 8, 2026
HomeLabaraiGwamnan Sokoto ya kara alawus ɗin NYSC zuwa Naira 20,000 a duk...

Gwamnan Sokoto ya kara alawus ɗin NYSC zuwa Naira 20,000 a duk wata

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince da ƙara kuɗin alawus ɗin da ake bai wa matasa masu yi wa ƙasa hidima NYSC daga naira 10,000 zuwa naira 20,000 a kowane wata.

Wannan ƙarin ya ninka kuɗin da matasan ke karɓa a baya, inda ake sa ran zai taimaka wajen rage musu matsin tattalin arziki a lokacin gudanar da shirin yi wa ƙasa hidima a jihar.

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da matasa masu yi wa ƙasa hidima ke fuskantar ƙalubalen tsadar rayuwa da sauran buƙatun yau da kullum.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments