Gabanin babban zaɓen shekarar 2027, an samu takun saƙa tsakanin gwamnatin Jihar Kano da rundunar ’yan sandan jihar, lamarin da ya shafi sauye-sauyen wuraren aikin wasu manyan jami’an rundunar.
Wani rahoto da jaridar Daily Nigerian ta wallafa ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi a sauya Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Bakori, tare da maye gurbinsa da CP Mohammed Yusuf Adamu, wanda aka ƙara wa girma kwanan nan.
Rahoton ya nuna cewa rashin jituwa tsakanin gwamnan da kwamishinan ’yan sandan ta samo asali ne daga yadda Bakori ya gudanar da sauye-sauyen wuraren aikin wasu jami’an rundunar, musamman waɗanda ke jagorantar ofisoshin ’yan sanda na ƙananan hukumomi da sassa daban-daban.
Majiyoyin da jaridar ta nakalto sun ce kwamishinan ya yi wasu naɗe-naɗe bisa la’akari da ƙwarewa da matsayin jami’ai, inda ya mayar da wasu manyan jami’ai masu mukamin CSP shugabannin sassan ’yan sanda, duk da cewa akwai wasu jami’ai masu irin wannan matsayi da ba su da wani takamaiman aiki a hedikwatar rundunar.
Wannan mataki dai bai samu karɓuwa daga wajen gwamnan ba, wanda ake zargin ya nemi a sake duba sauye-sauyen.
Haka kuma, rahoton ya ce Sufeto-Janar na ’yan sanda ya bayar da umarnin sauya wuraren aikin DPO 18 daga Kano zuwa wasu jihohi, ciki har da Yobe, Gombe, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Katsina.
Sai dai wata takarda mai ɗauke da ranar 15 ga Oktoba, 2026, da hedikwatar rundunar ta fitar, ta ƙunshi umarnin mayar da wasu jami’an da aka sauya zuwa tsoffin wuraren aikinsu, tare da wasu sababbin naɗe-naɗe.
Daga cikin ofisoshin ’yan sandan da sauye-sauyen suka shafa akwai Fagge, Gwale, Ungogo, Kumbotso, Sharada, Bompai da Bichi.
Batun ya sake buɗe ƙofa ga tambayoyi kan irin tasirin da gwamnati za ta iya yi a harkokin gudanarwar rundunar ’yan sanda, musamman a lokacin da ƙasar ke shirin tunkarar babban zaɓen 2027.
Ba wannan ne karon farko da ake danganta batun naɗe-naɗen kwamishinonin ’yan sanda da siyasar zaɓe a Kano ba.
A lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023 ma, jaridar Daily Nigerian ta taɓo zarge-zargen cewa tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, na ƙoƙarin ganin an naɗa kwamishinonin ’yan sanda da za su yi aiki da muradunsa.
Dangane da wannan sabon rahoto, kakakin rundunar ’yan sandan ƙasa, Anietie Iniedu, bai amsa kiran waya ko saƙon da aka aika masa domin jin ta bakinsa ba.
Shi kuwa kakakin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Mustapha Mohammed, ya ce ba shi da masaniya kan batun, don haka ba zai iya yin tsokaci a kai ba.