Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum da wasu mutane biyar da ke jigilar gawar matarsa daga Jihar Kano zuwa garinsu na Okpoga, da ke ƙaramar hukumar Okpokwu a Jihar Benue.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a daren Juma’a a yankin Adoka da ke ƙaramar hukumar Otukpo, inda maharan suka tafi da mutanen shida, suka bar gawar matar a cikin motar.
An gano motar a safiyar ranar Asabar, dauke da gawar matar, bayan da mazauna yankin suka lura cewa mutanen da ke cikinta sun ɓace.
Jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) sun isa wurin, inda suka dauki gawar zuwa ɗakin ajiyar gawa a garin Adoka.
Wani mai tasiri a kafafen sada zumunta na al’ummar Idoma, Meddy Olotu, ya ce masu garkuwar sun tuntubi iyalan waɗanda aka sace, inda suka nemi kuɗin fansa naira miliyan 15 domin sakin mutanen shida.
Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Prince Maxwell Ogiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici da tayar da hankali. Ya kuma tabbatar da cewa masu garkuwar na neman naira miliyan 15.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Benue, DSP Peter Aondongu, shi ma ya tabbatar da sace mutanen, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a.
Wannan shi ne karo na biyu cikin ƙasa da watanni biyar da aka samu rahoton sace mutanen da ke jigilar gawar wani ɗan uwansu a hanyar Otukpo–Ogobia–Adoka. A watan Yulin 2026, an sace wasu ’yan’uwa uku da ke jigilar gawar mahaifiyarsu daga Abuja zuwa Benue a wannan yankin.