Sunday, November 8, 2026
HomeLabaraiTinubu ya taya Flamingos murnar lashe kofin duniya, ya ce sun ɗaukaka...

Tinubu ya taya Flamingos murnar lashe kofin duniya, ya ce sun ɗaukaka martabar Najeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Flamingos, murnar lashe gasar cin kofin duniya ta mata ’yan ƙasa da shekara 17, bayan doke Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe da aka gudanar a Morocco.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Flamingos, murnar lashe gasar cin kofin duniya ta mata ’yan ƙasa da shekara 17, bayan doke Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe da aka gudanar a Morocco.

Tinubu ya bayyana nasarar a matsayin babban abin alfahari ga Najeriya da nahiyar Afirka, inda ya ce Flamingos ta kafa tarihi a matsayin tawaga ta farko daga Afirka da ta lashe kofin gasar.

A cikin saƙon taya murnar da ya wallafa, shugaban ƙasar ya ce ya tarar da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, tana kallon wasan ƙarshe yayin da suka dawo daga wasu ayyuka a jihohin Akwa Ibom da Rivers a yammacin ranar.

Ya ce ya bibiyi tafiyar tawagar a gasar, kuma yana tuna alƙawarin da ’yan wasan suka ɗauka bayan nasarar da suka samu a wasan kusa da na ƙarshe na cewa za su dawo da kofin gida. Ya ce sun cika wannan alƙawari ta hanyar jajircewa, ladabi da imani da kansu.

Tinubu ya ce nasarar za ta ƙarfafa gwiwar miliyoyin ’yan matan Najeriya su yi manyan mafarkai tare da cimma burinsu. Ya kuma taya ’yan wasan, masu horar da su, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), Hukumar Wasanni ta Ƙasa da duk waɗanda suka taimaka wajen samun nasarar murna, yana mai cewa sun rubuta sabon babi mai ɗaukaka a tarihin wasannin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments