Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana adadin ’yan Najeriya da gwamnatinsa ta fitar daga kangin talauci tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.
Obi ya kuma nemi shugaban ƙasar ya yi wa ’yan Najeriya bayani kan yadda aka kashe kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur, bashin da ya haura dala biliyan 100 da kuma ƙarin kuɗaɗen haraji.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa mai taken “Good Day, Mr President: Nigerians Deserve Accountability” da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar.
A cikin wasiƙar, Obi ya tambayi Tinubu adadin yaran da aka mayar makaranta, cibiyoyin kula da lafiya matakin farko da aka gina, da kuma matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen inganta wutar lantarki da tsaro a ƙasar.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga, ciki har da naira tiriliyan 15.8 da aka ce an samu daga cire tallafin man fetur, don haka ya kamata a ga tasirin kuɗaɗen a rayuwar al’umma.
Obi ya kuma tunatar da shugaban ƙasar alƙawarin da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe na cewa kada ’yan Najeriya su sake zaɓensa idan ya gaza magance matsalar wutar lantarki.
Ya jaddada cewa ’yan Najeriya na buƙatar sahihin bayani kan yadda aka sarrafa dukiyar ƙasar, yana mai cewa ya kamata a auna nasarar gwamnati da sauyin da aka samu a rayuwar al’umma.