Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ƙirƙirar wasu sabbin rumfunan zaɓe a wasu jihohi ya biyo bayan hukuncin kotu da ya haifar da kafa sabbin mazaɓu a jihohin Kogi, Benue da Delta.
Hakan na zuwa ne bayan rahotanni sun nuna cewa hukumar ta ƙara rumfunan zaɓe 453, lamarin da ya jawo tambayoyi kan gaskiya da bin ƙa’ida a shirye-shiryen zaɓen 2027.
Mataimakin daraktan yaɗa labarai na INEC, Wilfred Osilama Ifogah, ya bayyana cewa hukumar ba ta gudanar da aikin a ɓoye ba, amma za ta yi wa masu ruwa da tsaki bayani bayan kammala binciken cikin gida.
Ya ce kafa sabbin mazaɓu zai shafi wasu unguwanni da rumfunan zaɓe da ke yankunan da abin ya shafa, don haka hukumar na buƙatar tantance dukkan bayanai kafin sanar da cikakken bayani.
Ifogah ya bayyana cewa aikin ya bambanta da na shekarar 2020, lokacin da INEC ta mayar da wuraren kaɗa ƙuri’a zuwa rumfunan zaɓe domin rage cunkoso da sauƙaƙa wa masu zaɓe.
Sai dai har yanzu hukumar ba ta tabbatar da adadin rumfunan zaɓe 453 da aka ruwaito an ƙara ba, kuma ba ta fitar da cikakken bayani kan jihohi da wuraren da abin ya shafa ba.