Sunday, November 8, 2026
HomeSiyasaPeter Obi ya nemi Tinubu ya bayyana yadda aka kashe kuɗaɗen tallafin...

Peter Obi ya nemi Tinubu ya bayyana yadda aka kashe kuɗaɗen tallafin mai

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa ’yan Najeriya bayani kan yadda gwamnatinsa ta kashe kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, karɓar basussuka da kuma ƙarin kuɗaɗen haraji.

Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai taken “Good Day, Mr President: Nigerians Deserve Accountability”, inda ya taya Tinubu murnar shafe dare a Jihar Akwa Ibom, tare da buƙatar ya riƙa ziyartar sauran jihohin ƙasar domin ganawa kai tsaye da al’umma.

A cikin wasiƙar, Obi ya tambayi gwamnatin Tinubu yadda ta yi amfani da kuɗaɗen da ya ce sun kai Naira tiriliyan 15.8 da aka samu daga cire tallafin man fetur, sama da dala biliyan 100 da aka karɓo a matsayin bashi, da kuma ƙarin kuɗaɗen shiga daga haraji da sauran hanyoyin samun kuɗaɗen gwamnati.

Haka kuma, ya buƙaci gwamnati ta bayyana nasarorin da ta samu wajen rage talauci, rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inganta kiwon lafiya a matakin farko, samar da wutar lantarki da kuma tabbatar da tsaron ƙasa.

Obi ya kuma tuna wa Tinubu alƙawarinsa na cewa bai kamata ’yan Najeriya su sake zaɓensa ba idan ya gaza magance matsalar wutar lantarki, yana mai cewa al’umma na buƙatar cikakken bayani kan ci gaban da aka samu a wannan fanni.

Ya jaddada cewa Najeriya na buƙatar riƙon amana, gaskiya da kuma hujjojin da za su nuna cewa ana amfani da kuɗaɗen al’umma wajen inganta rayuwar talakawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments