Sunday, November 8, 2026
HomeTsaro“Kada a hana sojoji taimakawa idan tsaro ya fi karfin ’yan sanda”...

“Kada a hana sojoji taimakawa idan tsaro ya fi karfin ’yan sanda” – Gwamnatin Sokoto

Gwamnatin Jihar Sokoto ta yaba da shirin gwamnatin tarayya na janye sojoji a hankali daga ayyukan tsaron cikin gida, amma ta bukaci a gudanar da matakin cikin taka-tsantsan domin kauce wa sake faruwar matsalolin tsaro.

Mashawarci na musamman ga Gwamnan Jihar Sokoto kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Abdul Usman mai ritaya, ne ya bayyana hakan a wani bayani da ya fitar a Sokoto.

Usman ya yi wannan tsokaci ne bayan sanarwar Ministan Tsaro, Christopher Musa, cewa gwamnatin tarayya na shirin janye sojoji daga ayyukan tsaron cikin gida, tare da karfafa rundunar ’yan sanda.

Ya ce ya kamata sojoji su mayar da hankali wajen kare iyakokin ƙasa da kuma dakile manyan barazanar tsaro, kamar ta’addanci da tayar da ƙayar baya, yayin da ’yan sanda za su ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a cikin al’umma.

Sai dai ya jaddada cewa janye sojoji daga ayyukan tsaron cikin gida bai kamata ya hana su bayar da gudummawa ba idan matsalar tsaro ta fi ƙarfin ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments