Sunday, November 8, 2026
HomeSiyasa“Ku karɓi kuɗinsu, ku kashe, amma ku zaɓi wanda ku ka ga...

“Ku karɓi kuɗinsu, ku kashe, amma ku zaɓi wanda ku ka ga dama” – Makinde

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, kuma Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya shawarci magoya bayansa da su karɓi kuɗin da ’yan siyasa ke ba su, amma su yi zaɓe bisa ga ra’ayinsu.

Makinde ya ba da wannan shawara ne ranar Asabar, yayin wani gangamin neman zaɓen shugaban ƙasa da ya gudanar a Jihar Bauchi, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

A yayin gangamin, ya ce kada magoya bayansa su ji wani laifi saboda karɓar kuɗin da ’yan siyasa ke ba su, matuƙar za su yi zaɓe bisa ga ra’ayin zuciyarsu.

A kalamansa: “Kada ku damu ko kaɗan. Idan suka kawo kuɗi, kuɗinku ne, ku karɓa. Amma ku yi zaɓe bisa ga ra’ayin zuciyarku.
Kuma na san zuciyarku tana tare da mu da jam’iyyar APM.”

Gwamnan ya kuma yi alƙawarin sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya, tsarin tsaro da kuma yanayin zamantakewa da siyasar ƙasar idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Ya buƙaci ’yan Nijeriya da ba su gamsu da yadda ƙasar ke tafiya a halin yanzu ba, da su mara wa shirinsa na “Reset Nigeria” baya.

Makinde ya ce sake fasalin ƙasar ne kaɗai mafita ga matsalolin rashin adalci, rashin gaskiya da gazawar gwamnati wajen magance ƙalubalen al’umma. Ya kuma kira mutane da su kasance cikin waɗanda za su taimaka wajen kawo wannan sauyi.

A nasa jawabin, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar, Lawal Daura, ya ce siyasar ƙarya, yaudara da munafurci na barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya. Ya bayyana cewa shirin “Reset Nigeria” an tsara shi ne domin tunkarar waɗannan ƙalubale da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a gwamnati.

Shi ma shugaban jam’iyyar na ƙasa, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce shirin APM ya ƙunshi hanyoyin magance matsalolin da Nijeriya ke fuskanta.

Ya bayyana goyon bayansa ga takarar Makinde, yana mai cewa gwamnan ya nuna ƙwazo wajen gudanar da aiki da kuma tafiya da kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Gangamin ya samu halartar dimbin magoya bayan jam’iyyar da shugabanninta, waɗanda suka sanya tufafi masu launukan tambarin APM.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments