Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da tabbatar da gaskiya, SERAP, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta bayyana cikakken bayani kan yadda take samun kuɗaɗen tallafin Naira 50,000 da kuma yadda ake gudanar da shirin.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta bayyana sunayen ko bayanan waɗanda suka amfana da tallafin, tare da bayyana tsarin da ake bi wajen zaɓar mutanen da za su samu kuɗaɗen.
SERAP ta ce ya kamata gwamnati ta bayyana yadda ake amfani da kuɗaɗen shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention, domin ’yan Najeriya su samu damar sanin yadda ake tafiyar da shirin da kuma yadda ake kashe kuɗaɗensa.
Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin bayyana bayanan shirin ga jama’a domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da tallafin.