Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroNajeriya ba filin yaƙi ba ne – Obi ya yi tsokaci kan...

Najeriya ba filin yaƙi ba ne – Obi ya yi tsokaci kan hare-haren Neja

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya buƙaci gwamnatoci a dukkan matakai su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kansu tare da ɗaukar matakan gaggawa domin dakile ƙara ta’azzara matsalar tsaro a Najeriya.

Obi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, inda ya yi Allah-wadai da sabbin hare-haren da aka kai a wasu ƙauyuka da garuruwa a faɗin ƙasar.

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya ce hare-haren na baya-bayan nan da suka faru a jihohin Benue, Plateau da Neja na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa da kuma haɗin gwiwa daga hukumomin gwamnati.

Obi ya ce a Mangu, Jihar Plateau, an tabbatar da mutuwar akalla mutane 23 a harin Jwak Maitumbi, yayin da mazauna yankin suka ce adadin waɗanda suka mutu ya haura 30.

Ya ƙara da cewa an lalata gidaje sama da 45 a harin.

A Borgu, Jihar Neja kuwa, Obi ya ce rahotanni sun nuna cewa hare-haren baya-bayan nan sun yi sanadin mutuwar sama da mutane 40 tare da sace fiye da 100, sai dai ya ce akwai saɓanin adadin da ake bayarwa.

Ya ce hare-haren sun zo ne yayin da ake ci gaba da samun tashin hankali a Jihar Benue, inda al’ummomi ke fuskantar kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma lalata gidaje da wuraren noma.

Obi ya yi Allah-wadai da yadda hare-haren da garkuwa da mutane ke ƙara shafar ’yan Najeriya a wurare daban-daban, ciki har da wuraren ibada da gonaki.

Ya yi gargadin cewa bai kamata a riƙa kallon hare-haren da ake kai wa jihohi daban-daban a matsayin matsaloli ne na kowane yanki daban ba, domin abin da ke faruwa ya zama babbar matsalar tsaron ƙasa.

Obi ya ce:

“Najeriya ba ta cikin yaƙi a hukumance, amma ana kai wa ’yan ƙasa hari a ƙauyukansu, ana sace su bayan sun idar da ibada, ana korarsu daga gidajensu tare da kwace musu gonakinsu.”

Ya ce abin da ke faruwa a Benue, Plateau da Neja yana kama da abubuwan da ke faruwa a wasu sassan ƙasar, inda wasu hare-haren ma ba sa samun rahoto.

Ya buƙaci gwamnatin tarayya da sauran gwamnatoci su tashi tsaye wajen kare al’ummomin da ke cikin haɗari, inganta tattara bayanan sirri da kuma ƙarfafa tsarin kai ɗaukin gaggawa.

Haka kuma, ya nemi gwamnati ta ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da cafke waɗanda ke da hannu wajen kai hare-haren, a gurfanar da su a gaban kotu.

Obi ya ce bai kamata gwamnati ta ci gaba da jiran ana kashe mutane kafin ta ɗauki mataki ba.

Ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa shi ne babban nauyin gwamnati, yana mai cewa ya kamata a hana hare-haren kafin su faru.

Ya kara da cewa Najeriya ba za ta zama filin kashe-kashe ba, yana kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar tsaron.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments