Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciKamfanin OPay ya samu amincewa don shiga kasuwar hannayen jari ta Najeriya

Kamfanin OPay ya samu amincewa don shiga kasuwar hannayen jari ta Najeriya

Kamfanin hada-hadar kuɗi ta intanet na OPay ya samu amincewar shugabanninsa da masu hannun jari domin shiga kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX), bayan kammala shirin fara sayar da hannayen jarinsa a kasuwar New York.

Kamfanin hada-hadar kuɗi ta intanet na OPay ya samu amincewar shugabanninsa da masu hannun jari domin shiga kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX), bayan kammala shirin fara sayar da hannayen jarinsa a kasuwar New York.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin takardar rajista da ya miƙa wa Hukumar Kasuwannin Hannayen Jari ta Amurka (SEC) a ranar 9 ga Oktoba, 2026.

Matakin ya tabbatar da wani rahoto da Nairametrics ta fitar a baya cewa OPay na shirin shiga kasuwar Najeriya, abin da zai bai wa masu zuba jari a cikin gida damar mallakar hannun jari a kamfanin.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ranar fara cinikin hannayen jarin OPay a kasuwar NGX ba, domin shirin na buƙatar bin dokokin Najeriya da ƙa’idojin hukumomin da abin ya shafa.

OPay ta kuma yi gargaɗin cewa hannayen jarin da za a sayar a Najeriya ba za su kasance masu musanyawa kai tsaye da takardun hannun jarinta da ake cinikayya da su a kasuwar New York ba, sai an samar da tsarin da zai ba da damar musayar su tsakanin kasuwannin biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments