Tsohuwar ministar ilimi a Najeriya, Obiageli Ezekwesili, ta buƙaci masu ruwa da tsaki su ƙara zuba jari a ilimin ’ya’ya mata domin kawo ƙarshen auren wuri da ƙarfafa matsayinsu a cikin al’umma.
Ezekwesili ta bayyana cewa kusan mace ɗaya cikin biyar a duniya an aurar da ita kafin ta kai shekara 18, inda ta ce kimanin mata da ’yan mata miliyan 650 ke rayuwa a yau bayan an aurar da su tun suna ƙanana.
Ta ce a Najeriya, mata da ’yan mata miliyan 23.6 aka aurar da su kafin shekara 18, yayin da a jihar Jigawa kashi 78 cikin 100 na mata masu shekaru 20 zuwa 49 aka fara aurar da su tun kafin wannan shekarun.
Ezekwesili ta bayyana cewa auren wuri na jawo babbar asarar tattalin arziki da matsalolin lafiya, tana mai cewa rahoto ya kiyasta asarar da duniya ke yi har Dala biliyan 175 a kowace shekara sakamakon hakan.
Sai dai ta ce ana iya rage matsalar ta hanyar ilimin ’ya’ya mata, sauya dokoki da tallafin zamantakewa. Ta ƙara da cewa idan duk ’yan matan Afirka suka kammala karatun sakandare, za a iya kusan kawar da auren wuri gaba ɗaya.