Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya haura dala 110 kan kowace ganga a karon farko tun watan Mayun 2026, sakamakon fargabar ƙarin tsanantar rikicin Gabas ta Tsakiya da ka iya kawo cikas ga samar da mai.
A ranar Juma’a, farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya ƙaru da dala 3.94, kwatankwacin kashi 3.7 cikin ɗari, inda ya rufe kan dala 109.86 kan kowace ganga. Haka kuma, ɗanyen mai nau’in West Texas Intermediate (WTI) na Amurka ya ƙaru da dala 3.44, wato kashi 3.5 cikin ɗari, inda ya kai dala 101.41.
A cikin makon da ya gabata, farashin Brent ya ƙaru da kashi 4.9 cikin ɗari, yayin da WTI ya tashi da kashi 10.4 cikin ɗari.
Kamfanin bincike da ba da shawarwari kan makamashi na Energy Aspects ya ce farashin mai ya farfaɗo bayan fargabar sake tsanantar rikici ta ƙaru, sakamakon jita-jitar hare-hare kan wasu muhimman wuraren samar da makamashi a Saudiyya.