Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika, Reverend Father John Inalegwu Otache, a kan hanyar Otobi Amejo-Ajegbe da ke ƙaramar hukumar Ohimini a jihar Benue.
Rahotanni sun ce an sace limamin, wanda ke kula da cocin St. Margaret da ke Ajegbe-Awume, ranar Talata yayin da yake dawowa daga Otukpo.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, limamin cocin Otukpo, Reverend Father Joseph Aboyi Itodo, ya ce Bishop Michael Ekwoyi Apochi ya nuna matuƙar alhini kan lamarin, tare da kira ga Kiristoci da sauran al’umma su yi addu’ar samun kubutar limamin cikin ƙoshin lafiya.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana ƙoƙarin ganin an kuɓutar da limamin, wanda wannan ne karo na biyu da aka sace wani limami mai aiki a cocin St. Margaret da ke Ajegbe-Awume.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Benue, DSP Peter Aondongu, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto limamin, wanda har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a kuɓutar da shi ba.