Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSheikh Jingir: Ban taba kin Kiristoci ba, kalaman da ake danganta ni...

Sheikh Jingir: Ban taba kin Kiristoci ba, kalaman da ake danganta ni da su zargi ne kawai

Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya musanta zargin cewa ba ya son Kiristoci, yana mai cewa kalaman da ake danganta masa a kan hakan ba su wuce “zargi kawai” ba.

Sheikh Jingir ya bayyana hakan ne a yayin wani taron yini guda na ƙasa da aka gudanar a Jos, mai taken “Enhanced Political Participation and Social Justice as a Panacea for Unity and Development in Nigeria.”

An shirya taron ne domin wayar da kan mambobin JIBWIS kan muhimmancin shiga harkokin siyasa cikin hikima, musamman gabanin zaɓukan ƙasar.

Sheikh Jingir ya ce kalaman da ya yi a wajen bikin auren ma’aurata 1,500 da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya ba su da nufin nuna ƙiyayya ga Kiristoci ko wasu waɗanda ba Musulmai ba.

Ya ce:

“Mutane da yawa suna cewa ba na son Kiristoci. Ban ce ba na son Kiristoci ba. Ƙarya ce. An fahimci kalamaina ba daidai ba.”

Malamin ya ƙara da cewa koyarwar Musulunci ba ta amince da yaudara ko zaluntar mutanen da suke da addini daban ba.

A cewarsa, Musulunci yana koyar da nuna ƙauna da kyakkyawar mu’amala ga mutane masu addinai ko mazhabobi daban-daban.

Sheikh Jingir ya kuma bayyana cewa duk Musulmin da ya yaudari ko ya zalunci wanda ba Musulmi ba za a tambaye shi a ranar Alƙiyama, yana mai cewa Annabi Muhammad (SAW) ya rayu cikin zaman lafiya da waɗanda ba Musulmai ba.

Ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da sauran shugabannin ƙasar da su yi adalci ga kowa, ba tare da la’akari da ƙabila, addini ko jam’iyyar siyasa ba.

Ya buƙaci shugabanni su guji zaluntar Musulmi da waɗanda ba Musulmai ba, sannan su mutunta ’yan Najeriya da ba sa cikin jam’iyyarsu.

Sheikh Jingir ya kuma jaddada cewa kowane ɗan Najeriya na da ’yancin zaɓar ɗan takarar da yake ganin ya dace da shi a lokacin zaɓe.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da zama tare, yana mai cewa babu ci gaba ba tare da zaman lafiya ba.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027 domin ya kammala wa’adin shekaru takwas, kamar yadda wanda ya gabace shi daga Arewa ya yi.

Barau ya bayyana tsarin karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu a matsayin wani muhimmin ginshiƙi wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Ya ce goyon bayan Tinubu a wa’adi na biyu ba wai batun Tinubu kaɗai ba ne, illa batun cika fahimtar siyasa da aka yi tsakanin Arewa da Kudu.

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, da Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments