Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroGwamna Bago ya umarci a ceto masallatan da yan bindiga su ka...

Gwamna Bago ya umarci a ceto masallatan da yan bindiga su ka yi awon gaba da su

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana matuƙar damuwa da lamarin, tare da yin Allah-wadai da harin.

Gwamnan ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su haɗa kai da jami’an tsaro domin ganin an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su cikin gaggawa.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin dakile ayyukan masu aikata laifuka.

A cewar gwamnatin, an tura rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin domin tantance halin da ake ciki, bin sawun maharan da kuma ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.

Sai dai gwamnati ta ce ba za ta bayyana cikakkun bayanai kan wuraren da jami’an tsaro suke aiki ko kuma dabarun da suke amfani da su ba, saboda yanayin aikin ceto da ake gudanarwa.

Gwamnatin Neja ta buƙaci jama’a, musamman mazauna yankin Borgu, da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba game da harin.

Ta ce yaɗa adadin waɗanda aka kashe ko aka sace ba tare da tabbatar da hakan daga hukumomin da suka dace ba na iya ƙara tayar da hankalin jama’a tare da kawo cikas ga ayyukan jami’an tsaro.

Gwamna Bago ya kuma yaba wa al’ummar Borgu bisa ƙarfin hali da juriyar da suka nuna, yana mai tabbatar musu da cewa tsaro da kare rayukan al’ummar Neja na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Lamarin ya sake janyo damuwa kan matsalar hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane da ke ci gaba da addabar wasu yankunan Jihar Neja.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments