Abdullahi Abubakar, mai shekaru 30, ya fara ganin haske bayan shafe shekaru 27 yana fama da makanta. An yi masa tiyatar ido a asibitin Makkah Specialists Eye Hospital da ke Kano makonni bakwai da suka gabata.
Abdullahi, wanda aka haifa a Jihar Kebbi amma ya girma a Wudil ta Kano, ya ce ya rasa ganinsa tun yana ɗan shekara uku. Duk da ƙalubalen da ya fuskanta, ya yi sana’o’i daban-daban, ciki har da sayar da ruwa da dabbobi.
Ya ce likitoci sun tabbatar da cewa za a iya dawo masa da gani ta hanyar tiyatar da za ta ci Naira 180,000, amma ya kasa samun kuɗin. Daga bisani, shugaban ƙaramar hukumar Wudil ya ɗauki nauyin yi masa tiyatar.
Abdullahi ya ce babban farin cikinsa shi ne ganin fuskar ’yarsa a karon farko, tare da ganin fuskarsa ta kyamarar wayarsa. Ya kuma bayyana jin daɗinsa na kallon kogin Wudil da taurari a sararin sama.
Bayan tiyatar, shugaban ƙaramar hukumar ya ba shi Naira 100,000 domin fara sana’a. Abdullahi ya ce yana son komawa cinikin dabbobi, sannan ya fara koyon karatu da rubutu domin amfani da sabuwar damar da ya samu.