A rana irin ta yau 14 ga watan Oktoba, Shekarar 1947, matukin jirgin sama ɗan ƙasar Amurka, Chuck Yeager, ya kafa tarihi bayan ya yi nasarar tuƙa jirgin gwaji mai suna Bell X-1 da gudun da ya zarce saurin sauti, lamarin da ya zama wani gagarumin ci gaba a tarihin kimiyya da fasahar zirga-zirgar jiragen sama.
Kafin wannan nasara, masana kimiyya da injiniyoyin jiragen sama suna fuskantar ƙalubalen yadda za su ƙera jirgin da zai iya wuce saurin sauti ba tare da ya samu matsala ba.
A lokacin, akwai fargabar cewa matsin iska da jirgi ke fuskanta yayin da yake kusantar saurin sauti zai iya haddasa rashin daidaituwar jirgi ko ma lalacewarsa.
Domin shawo kan wannan ƙalubale, kamfanin Bell Aircraft na Amurka ya ƙera jirgin gwaji mai suna Bell X-1. An tsara jirgin da sifar harsashin bindiga domin taimaka masa ratsa iska cikin sauƙi yayin da yake tafiya da babban gudu.
A ranar 14 ga Oktoba, 1947, wani babban jirgin sama mai suna B-29 ya ɗauki Bell X-1 zuwa sararin samaniya, kafin a sake shi domin ya ci gaba da tashi ta amfani da injin roket ɗinsa.
Chuck Yeager ne ya jagoranci wannan gwaji, inda ya samu nasarar tuka jirgin da gudun da ya kai kusan Mach 1.06, wato sama da saurin sauti.
Wannan nasara ta tabbatar da cewa jirgin sama mai matuƙi zai iya wuce saurin sauti, tare da kawo ƙarshen wasu shakku da ake da su a lokacin game da yiwuwar cimma wannan buri.
Nasarar Yeager ta buɗe sabon babi a tarihin zirga-zirgar jiragen sama, inda ta taimaka wajen bunƙasa binciken kimiyya da ƙera jiragen sama masu saurin gaske, ciki har da jiragen yaƙi na zamani.
Haka kuma, gwajin ya taimaka wajen ƙara fahimtar yadda iska ke mu’amala da jiragen sama yayin da suke tafiya da gudun da ya zarce saurin sauti, wanda ya zama muhimmin ginshiƙi wajen ci gaban fasahar jiragen sama a shekarun da suka biyo baya.
A yau, ana tunawa da Chuck Yeager a matsayin ɗaya daga cikin fitattun matukan jiragen gwaji a tarihi, yayin da nasarar da ya samu a shekarar 1947 ta kasance wani muhimmin ci gaba a fannin kimiyya da fasahar zirga-zirgar jiragen sama.
tarihi ya nuna yadda jajircewa, bincike da ƙirƙire-ƙirƙire za su iya karya shingayen da a da ake ganin ba za a iya ketarewa ba.