Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiGwamna Dauda Lawal ya sanya hannu kan sabbin dokokin ilimi a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya sanya hannu kan sabbin dokokin ilimi a Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan wasu sabbin dokokin zartarwa da nufin inganta tsarin ilimi a jihar, tare da ƙaddamar da rabon daftarin manhajar karatu ta ƙasa ga makarantun gwamnati.

Sabbin dokokin sun shafi inganta tafiyar da makarantu, kare makarantu, lafiyar ɗalibai, tsaro, ciyar da ɗalibai, da kuma tabbatar da amintaccen sufuri zuwa makarantu.

Gwamna Lawal ya bayyana cewa ilimi shi ne ginshiƙin rage talauci, samar da zaman lafiya, ƙarfafa tsaro da bunƙasa tattalin arziki.

Ya ce gwamnatin Zamfara za ta ci gaba da saka hannun jari a fannin ilimi domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga ɗaliban jihar.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Zamfara, Abdulmalik Abubakar Gajam, ya ce nasarar waɗannan sauye-sauye za ta dogara ne da haɗin gwiwar gwamnati, malamai, iyaye, al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments