Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta shirya tsaf domin kafa yan sandan Jiha

Gwamnatin Kano ta shirya tsaf domin kafa yan sandan Jiha

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kammala shirye-shiryen da suka dace domin aiwatar da tsarin ’yan sandan jiha, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar Hukumomi Kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano.

A cewar gwamnan, sabon tsarin ba zai maye gurbin rundunar ’yan sandan Najeriya ba, illa zai kasance wata hanya ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin magance matsalolin tsaro cikin sauri da inganci.

Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar da za a samu tsakanin ‘yan sandan jiha da sauran hukumomin tsaro zai inganta tattara bayanan sirri, hanzarta mayar da martani ga barazanar tsaro, tare da ƙara amincewar jama’a ga jami’an tsaro.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta nuna cewa gwamnatin Kano na ci gaba da ɗaukar matakan da za su tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma a faɗin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments