Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya sallami kwamishinoni 6 a Jihar

Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya sallami kwamishinoni 6 a Jihar

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sallami kwamishinoni shida a wani sauyi da ya ce an yi domin ƙara inganta aikin gwamnati gabanin zaɓen 2027.

Gwamnan ya bayyana cewa matakin ba rushe majalisar zartarwa baki ɗaya ba ne, kamar yadda wasu rahotanni suka nuna, illa dai wani sauyi ne na dabarun gudanar da mulki domin ƙarfafa shugabanci da hanzarta aiwatar da manufofin gwamnati.

Ma’aikatun da abun ya shafa sun haɗa da:

Tsaro da Harkokin Musamman, Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma, Ayyuka, Sufuri da Gidaje, Kimiyya da Fasaha, Yaɗa Labarai, Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Filaye da Binciken Ƙasa.

Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa, Shuaibu Magaji (SAN), ya ce za a sanar da sunayen sabbin kwamishinoni bayan kammala dukkan matakan da suka dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments