Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiArewa House ta soke izinin gabatar da littafin da ya soki gwamnatin...

Arewa House ta soke izinin gabatar da littafin da ya soki gwamnatin Tinubu a Kaduna

Hukumar gudanarwar Arewa House ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta janye amincewar da ta bayar na kaddamar da wani littafi da ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tana mai cewa hakan ya samo asali ne daga wasu buƙatun gudanarwa.

Hukumar gudanarwar Arewa House ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta janye amincewar da ta bayar na kaddamar da wani littafi da ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tana mai cewa hakan ya samo asali ne daga wasu buƙatun gudanarwa.

Sai dai marubucin littafin, Abubakar Siddique Mohammed, ya zargi wasu da ƙoƙarin hana taron gudana, yana mai cewa an kuma samu matsala wajen neman wani wurin taro a Kaduna.

An shirya gabatar da littafin mai suna Tinubu: From Renewed Hope to Despair a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, amma Arewa House ta ce za ta buƙaci wurin domin gudanar da bincike, gyare-gyare da shirye-shiryen bayan jarrabawa.

Mohammed, wanda shi ne babban daraktan CEDDERT, ya ce yanzu sun yanke shawarar mayar da taron zuwa Abuja, inda za su sanar da sabon wuri da ranar gudanar da shi. Ya kuma bayyana cewa bai kamata a hana jama’a tattaunawa kan manufofin gwamnati ba.

A nata ɓangaren, Amnesty International ta yi Allah-wadai da soke taron, tana mai bayyana matakin a matsayin barazana ga ’yancin faɗar albarkacin baki. Ƙungiyar ta buƙaci Jami’ar Ahmadu Bello ta janye matakin tare da kare ’yancin bayyana ra’ayi da gudanar da muhawara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments