Ƙungiyar Afenifere ta bayyana damuwa kan ƙaruwar rashin haƙuri, kalaman tunzura jama’a da rashin ɗa’a tsakanin ’yan siyasar Najeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A taronta na kwamitin zartarwa na ƙasa da ta gudanar a Legas, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa kalaman siyasa marasa daɗi na ƙara tayar da hankula tare da barazana ga dimokuraɗiyyar ƙasar.
Afenifere ta kuma buƙaci ’yan siyasa daga dukkan jam’iyyu su kasance masu natsuwa da mutunta juna, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da ’yancin hukumar zaɓe ta INEC a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta soki yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke tafiyar da tattalin arziki, tana mai cewa yunwa, wahalar rayuwa da hauhawar farashi sun zama manyan matsalolin ƙasar.
Haka kuma, Afenifere ta yi watsi da matakin sanya farashin fetur a kan Naira 1,350 kan kowace lita, tana neman a rage shi zuwa tsakanin Naira 350 da 400. Ta kuma buƙaci ƙarin mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, tana mai cewa hauhawar farashi ta rage masa tasiri.