Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShekaru 22 da suka wuce, Adams Oshiomhole ya jagoranci zanga zangar NLC...

Shekaru 22 da suka wuce, Adams Oshiomhole ya jagoranci zanga zangar NLC kan farashin fetur

A ranar 11 ga Oktoba, 2004, tsohon shugaban Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Adams Oshiomhole, ya jagoranci zanga-zangar ma’aikata a Abuja, a matsayin wani ɓangare na yajin aikin gama-gari na ƙasa baki ɗaya domin nuna adawa da ƙarin farashin fetur.

Yajin aikin na kwanaki huɗu ya fara ne bayan gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo ta ƙara farashin man fetur da kusan kashi 25 cikin 100 a watan Satumba na shekarar 2004. Ƙungiyar NLC ta buƙaci gwamnati ta janye ƙarin farashin, tana mai cewa hakan na ƙara wa ’yan Najeriya wahalar rayuwa.

Yayin da aka fara yajin aikin, Oshiomhole ya zargi gwamnatin tarayya da ƙin tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago duk da wa’adin makonni biyu da suka bayar domin a warware matsalar. Ma’aikata da ƙungiyoyin fararen hula sun shiga zanga-zangar a sassa daban-daban na ƙasar.

Yajin aikin ya jawo rufe bankuna, makarantu, ofisoshi da shaguna a manyan birane kamar Legas, Ibadan, Kano da Fatakwal. A wasu wurare, an samu arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga, yayin da rahotanni suka ce mutane biyu sun mutu a rikicin da ya faru a Kaduna da Fatakwal.

An dakatar da yajin aikin a ranar 14 ga Oktoba, bayan kwashe kwanaki huɗu, domin bai wa gwamnati ƙarin makonni biyu ta sake duba ƙarin farashin. Sai dai shugabannin ƙwadago sun yi gargaɗin cewa za su sake komawa yajin aiki idan gwamnati ta ƙi janye ƙarin farashin fetur.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments