Matatar man fetur ta Dangote ta sake jawo hankalin duniya bayan ta samu gagarumar nasara wajen fitar da man jiragen sama zuwa nahiyar Turai.
Rahotanni sun nuna cewa a watan Yunin 2026, matatar ta fitar da kimanin tan 466,000 na wannan nau’in mai, abin da aka kiyasta darajarsa ta haura Naira biliyan 757.
Wani bincike da kamfanin S&P Global Commodity Insights ya gudanar ya nuna cewa wannan ci gaba ya bai wa Najeriya damar zarce Amurka a matsayin ƙasar da ta fi samar da man jiragen sama ga kasuwar Turai a cikin watan Yuni na shekarar 2026.
Alƙaluman sun nuna cewa yawan man jiragen saman da Najeriya ta fitar zuwa Turai ya ƙaru sosai daga tan 232,000 a watan Mayu zuwa tan 466,000 a watan Yuni.
Wannan ya nuna yadda matatar Dangote ke ci gaba da faɗaɗa ayyukanta da kuma ƙarfafa matsayin Najeriya a kasuwar makamashi ta duniya.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa wannan shi ne mafi girman adadin man jiragen sama da Najeriya ta taɓa fitarwa zuwa Turai tun bayan da ƙasar ta fara fitar da wannan nau’in mai fiye da yadda take shigo da shi a shekarar 2024.
Jimillar man da aka fitar a watan Yuni ta kai kusan lita miliyan 582.5, wanda aka kiyasta darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757.25.
A gefe guda kuwa, bayanan sun nuna cewa fitar da man jiragen sama daga Amurka zuwa Turai ya ci gaba da raguwa a watannin baya-bayan nan.