Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTarihiA rana irin ta yau aka fara bikin cika shekaru 2500 da...

A rana irin ta yau aka fara bikin cika shekaru 2500 da kafuwar daular Farisa

A rana irin Yau 12 ga watan Oktoba, 1971, aka fara bikin cika shekaru 2500 da kafuwar Daular Farisa, wadda a yau ake kira Iran.

An gudanar da gagarumin bikin ne a Persepolis, kusa da kabarin Cyrus, daga ranar 12 zuwa 14 ga Oktoba, 1971. Bikin ya samu halartar manyan shugabannin ƙasashe da baƙi daga sassa daban-daban na duniya.

An danganta kafuwar Daular Farisa da zamanin Cyrus, wanda ya kafa daula mai faɗi da tasiri a kusan shekara ta 550 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Daular ta taka muhimmiyar rawa a tarihin siyasa, al’adu da wayewar kai a duniya.

Bikin ya kasance wata hanya ta tunawa da tsohon tarihin Iran da kuma nuna irin gudummawar da Daular Farisa ta bayar wajen gina ɗaya daga cikin manyan daulolin duniya a zamanin da.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments