Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaRikici na shirin kunno kai a Jam’iyyar NDC kan zaben yan takara

Rikici na shirin kunno kai a Jam’iyyar NDC kan zaben yan takara

Ƙungiyar yankin Kudu maso Gabas ta jam’iyyar NDC ta bukaci shugabannin jam’iyyar na ƙasa da su gaggauta bayyana sakamakon zaɓen fidda gwani tare da gujewa duk wani yunƙurin kakaba ‘yan takara.

Ƙungiyar ta ce irin wannan mataki na iya haddasa rikici a cikin jam’iyyar tare da kawo cikas ga shirye-shiryenta na babban zaɓen shekarar 2027.

Wannan kira na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke kokarin cika wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta gindaya na miƙa sunayen ‘yan takararsu domin tunkarar zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta jaddada cewa bin tsarin dimokuraɗiyya shi ne ginshiƙin tabbatar da adalci da haɗin kai a cikin jam’iyya.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, shugaban NDC na yankin Kudu maso Gabas a FCT, Maxwell Igbokwe, ya buƙaci shugabancin jam’iyyar ya mutunta kundin tsarin mulki tare da tabbatar da cewa waɗanda suka yi nasara a sahihin zaɓen fidda gwani ne kaɗai za a miƙa sunayensu ga INEC.

Ya kuma nuna damuwa kan jinkirin sanar da sakamakon wasu zaɓukan da aka gudanar fiye da watanni biyu da suka gabata.

Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa an samu kura-kurai da kuma yunƙurin sauya sakamakon zaɓen fidda gwani na kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar AMAC/Bwari da ke Abuja.

A cewarta, hakan ya sa wasu mambobi ke fargabar cewa ana ƙoƙarin maye gurbin wanda ya samu nasara ta hanyar da ba ta dace ba.

NDC ta ce an kafa jam’iyyar ne domin tabbatar da gaskiya, adalci da dimokuraɗiyya ta gaskiya, don haka ta yi kira ga shugabanninta da su kiyaye waɗannan manufofi.

Ƙungiyar ta yi gargadin cewa duk wani yunƙurin karya tsarin zaɓen cikin gida na iya haifar da rashin haɗin kai da kuma raunana jam’iyyar kafin zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments