Tauraron ƙwallon ƙafa na Portugal, Cristiano Ronaldo, ya ce har yanzu bai tabbatar ko wasan da ya buga ne zai zama na ƙarshe da zai wakilci tawagar ƙasarsa ba.
Ronaldo ya bayyana cewa ba ya yanke manyan hukunci cikin gaggawa ko bisa yanayi na rashin jin dadi, yana mai cewa irin waɗannan hukunce-hukunce na buƙatar nutsuwa da yin dogon nazari.
Ya ce a halin yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne tawagar Portugal da abin da ta cimma, ba batun makomarsa ta kansa ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa idan lokaci ya yi da zai yanke hukunci kan ci gaba da bugawa Portugal ko yin ritaya daga buga wa ƙasa wasa, zai sanar da magoya baya.
Kalaman na Ronaldo sun ƙara jawo muhawara kan makomarsa a tawagar Portugal, yayin da magoya baya ke ci gaba da jiran ko zai ci gaba da taka leda a matakin ƙasa ko kuma ya kawo ƙarshen aikinsa na ƙasa.