Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciNajeriya ta shigo da tuffa da inibi na Naira biliyan 33 cikin...

Najeriya ta shigo da tuffa da inibi na Naira biliyan 33 cikin watanni shida

Najeriya ta shigo da tuffa da inibi da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 33.03 a farkon watanni shida na shekarar 2026, a cewar bayanan Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS).

Najeriya ta shigo da tuffa da inibi da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 33.03 a farkon watanni shida na shekarar 2026, a cewar bayanan Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS).

Rahoton ya nuna cewa an shigo da tuffa ta Naira biliyan 10.38 a zangon farko, yayin da a zangon na biyu aka shigo da tuffa da inibi na Naira biliyan 22.65, galibinsu daga Afirka ta Kudu.

Tsohon shugaban ƙungiyar manoman Najeriya (AFAN), Mohammed Gettado, ya ce ana noman tuffa a jihar Filato, amma ana samar da ita kaɗan saboda rashin tallafin gwamnati da kuma ra’ayin cewa ’ya’yan itacen na masu kuɗi ne kawai.

Gettado ya ce samar da ingantattun iri, taki da sauran kayan noma a kan lokaci, tare da samun kasuwanni, zai taimaka wajen bunƙasa noman tuffa a Najeriya.

A ɓangaren inibi, Deola Balogun ta kamfanin Limlim Foods ta ce tsadar sufuri da zafi na jawo asarar amfanin gona, musamman wajen jigilar su daga Jos. Ta ce a wani yunƙuri, sun yi asarar kashi 20 zuwa 30 cikin ɗari na inibi saboda jinkiri da zafi, tana mai cewa inganta sufuri zai taimaka wajen rage shigo da su daga ƙasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments