Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiGwamnatin Zamfara ta dage komawar makarantu saboda yaduwar cutar mashako

Gwamnatin Zamfara ta dage komawar makarantu saboda yaduwar cutar mashako

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da tsawaita ranar komawar ɗalibai makarantun gwamnati da masu zaman kansu da mako biyu, sakamakon yaɗuwar cutar mashako, wato diphtheria, a jihar.

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Abdulmalik Abubakar Gajam, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kan halin da ake ciki.

A cewarsa, an ɗauki matakin ne bisa shawarwarin hukumomin kiwon lafiya, domin kare rayuka da lafiyar ɗalibai, malamai da sauran al’ummar makarantu.

Ya ce ƙarin lokacin zai bai wa hukumomin lafiya da na ilimi damar gudanar da bincike, bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da masu ɗauke da cutar, da tabbatar da gudanar da rigakafi yadda ya kamata.

Haka kuma, gwamnatin za ta ƙara wayar da kan jama’a tare da ɗaukar sauran matakan kariya kafin a sake buɗe makarantun domin ci gaba da karatu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments