Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroKebbi: Masu zanga-zanga sun tare hanyar Jega zuwa Kontagora kan matsalar tsaro

Kebbi: Masu zanga-zanga sun tare hanyar Jega zuwa Kontagora kan matsalar tsaro

Wasu mazauna jihar Kebbi sun tare babbar hanyar Jega zuwa Kontagora domin nuna fushinsu kan ƙara tabarbarewar tsaro da hare-haren da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne ke kai wa al’ummominsu.

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna masu zanga-zangar suna cinna wa tayoyi wuta a kan hanyar, yayin da jami’an ’yan sanda suka yi ƙoƙarin tarwatsa su ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye.

Rahotanni sun bayyana cewa zanga-zangar ta haifar da tsaiko a zirga-zirgar ababen hawa, inda direbobi da matafiya suka shafe sa’o’i da dama a makale kafin daga bisani aka sake buɗe hanyar.

Wani mazaunin Jega, Nazeer Muhammad, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa hare-haren da ake kai wa wasu ƙauyuka sun tilasta wa mazauna yankunan barin gidajensu domin neman mafaka a wuraren da suka fi samun tsaro.

Ya ce garin Jega ya cika da mutanen da suka rasa matsugunansu, inda wasu daga cikinsu ke kwana a fili saboda rashin wuraren zama.

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda suka rasa matsugunansu sun fito ne daga al’ummomin Mayama da Ungushi da ke jihar Sakkwato.

Shi ma wani mazaunin Jega da ya bayyana sunansa da Malam Idris kawai, ya ce a ranar Lahadi, manyan motoci guda takwas ɗauke da mutanen da suka rasa matsugunansu sun isa garin.

Lamarin ya ƙara jawo hankalin jama’a kan halin da mazauna yankunan da ke fama da hare-hare ke ciki, musamman waɗanda aka tilasta wa barin gidajensu saboda matsalar tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments