Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZulum: Bayan wa’adin Tinubu, mulkin Najeriya zai koma Arewa

Zulum: Bayan wa’adin Tinubu, mulkin Najeriya zai koma Arewa

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce shugabannin Arewacin Najeriya sun amince da bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikakken goyon baya domin sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa bayan kammala wa’adinsa shugabancin ƙasar zai koma Arewa.

Zulum ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Kaduna, bayan wata ganawa da shugabannin mata malamai da malaman addinin Musulunci daga sassan Arewacin Najeriya.

A cewarsa, wannan fahimtar siyasa ta samo asali ne domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin yankunan Arewa da Kudancin Najeriya. Ya ce Arewa ta taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Tinubu a zaɓen 2023, don haka akwai buƙatar mutunta fahimtar da aka cimma tsakanin yankunan ƙasar.

Gwamnan ya kuma bukaci ’yan Najeriya su ƙara haƙuri tare da bai wa gwamnatin tarayya goyon baya wajen magance matsalolin rashin tsaro, talauci da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce shugabannin Arewa sun tattauna kan matsalolin tsaro, ƙaruwar yara da ba sa zuwa makaranta da kuma talauci, tare da ɗaukar matakan da za su taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.

Zulum ya kuma yi kira ga mata malamai da su ƙara himma wajen yaɗa saƙon zaman lafiya da haɗin kai, yana mai jaddada muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen tarbiyyar yara da gina al’umma.

Ya jaddada cewa bai kamata siyasa ta zama sanadin tayar da rikici ko raba kan jama’a ba, tare da kira ga ’yan Najeriya su haɗa kai domin magance matsalolin da ke addabar ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments