Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da tsawaita ranar komawar ɗalibai makarantun gwamnati da masu zaman kansu da mako biyu, sakamakon yaɗuwar cutar mashako, wato diphtheria, a jihar.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Abdulmalik Abubakar Gajam, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kan halin da ake ciki.
A cewarsa, an ɗauki matakin ne bisa shawarwarin hukumomin kiwon lafiya, domin kare rayuka da lafiyar ɗalibai, malamai da sauran al’ummar makarantu.
Ya ce ƙarin lokacin zai bai wa hukumomin lafiya da na ilimi damar gudanar da bincike, bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da masu ɗauke da cutar, da tabbatar da gudanar da rigakafi yadda ya kamata.
Haka kuma, gwamnatin za ta ƙara wayar da kan jama’a tare da ɗaukar sauran matakan kariya kafin a sake buɗe makarantun domin ci gaba da karatu.