Saturday, November 14, 2026
HomeLabaraiLabaraiBanga: Tinubu ya gargadi yan siyasa gabanin zaben 2027

Banga: Tinubu ya gargadi yan siyasa gabanin zaben 2027

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani nau’in tashin hankali da rikicin siyasa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Shugaban ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa a yayin tarukan siyasa a sassa daban-daban na ƙasar.

Tinubu ya bayyana cewa ya kamata ’yan siyasa su mayar da hankali wajen gabatar da manufofi da ra’ayoyin da za su kawo ci gaba da inganta rayuwar al’umma, maimakon shiga rikici.

Haka kuma, ya buƙaci jami’an tsaro da su ɗauki tsauraran matakai kan duk wanda aka samu da hannu wajen haddasa rikicin siyasa.

Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan jerin hare-haren da aka kai wa wasu ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyu a jihohi daban-daban.

A Gombe, wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan ayarin motocin tsohon minista, Isa Pantami.

A Sakkwato kuwa, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC, Mannir Ɗan’iya, ya zargi jami’an tsaro da kai hari kan ayarin motocinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments