Saturday, November 14, 2026
HomeLabaraiKotun ta daure mai 'aljani' mai barazanar shanye jinin wata budurwa idan...

Kotun ta daure mai ‘aljani’ mai barazanar shanye jinin wata budurwa idan ta ki jima’i da shi

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jogana, Kano, ta bayar da umarnin a tsare wani mutum mai suna Musa Haruna Rangaza a gidan gyaran hali har zuwa ranar 24 ga Nuwamba, 2026, bayan ya amsa laifin tsoratar da wata budurwa tare da yi mata barazanar shanye jininta.

Ya rika yi mata barazana da cewa shi aljani ne.

Tun da farko, wata matashiya mai suna Hafsat Aliyu, mazauniyar unguwar Dakata, ta shigar da ƙorafi a ofishin ‘yan sanda, inda ta zargi Musa da yawan kiranta ta waya yana barazanar cewa yana da wani aljani da zai iya kamo ta a duk inda take idan ta ƙi amincewa da buƙatarsa na saduwa da ita.

Ta kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin yana aiki ne da wata ƙungiyar asiri.

Bayan kammala bincike, ‘yan sanda sun gurfanar da Musa Haruna Rangaza a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jogona, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Kamalu Haruna Durumin Iya.

An tuhumi wanda ake zargin ne da aikata laifin tsoratarwa da kuma barazanar aikata laifi.

Mai gabatar da ƙara, Insifekta Murtala Kabara, ne ya karanta masa tuhume-tuhumen da ake yi masa, inda nan take ya amsa laifin.

Bayan haka, masu gabatar da ƙara sun roƙi kotun da ta ɗage sauraron batun yanke hukunci zuwa zama na gaba saboda ƙarancin lokaci.

Kotun ta bayar da umarnin a tsare Musa a gidan gyaran hali har zuwa ranar 24 ga Nuwamba, 2026, lokacin da za ta yanke masa hukunci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments