Saturday, November 14, 2026
HomeSiyasaADC ta bukaci Tinubu ya janye kalamansa kan siyasa, ya rungumi zaman...

ADC ta bukaci Tinubu ya janye kalamansa kan siyasa, ya rungumi zaman lafiya

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fito fili ya janye kalamansa na cewa “All Is Fair in Politics” (komai ya halatta a siyasa), tana mai cewa irin waɗannan kalamai na iya ƙara rura wutar rikicin siyasa da barazana ga zaman lafiyar ƙasar.

Haka kuma, kwamitin ya nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin shirun shugaban ƙasar game da wasu gwamnonin APC da shugabannin jam’iyyar da take zargi da yin kalaman tunzura jama’a da kuma ƙarfafa tashin hankali.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC-PCC ta buƙaci Tinubu da ya fifita muradun ƙasa sama da na jam’iyyarsa, yana mai nuna halin shugabanci na gari.

Kwamitin ya yi nuni da kalaman tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan na cewa babu wata buƙatar neman shugabancin ƙasa da ta kai darajar jinin ɗan Najeriya.

ADC-PCC ta kuma soki abin da ta kira gazawar Tinubu wajen yin Allah-wadai da ƙaruwar rikicin siyasa, tana mai zargin fadar shugaban ƙasa da mayar da hankali wajen jan kunnen jam’iyyun adawa maimakon kiran waɗanda ake zargi da haddasa rikici a jam’iyyar APC.tana mai zargin fadar shugaban ƙasa da mayar da hankali wajen jan kunnen jam’iyyun adawa maimakon kiran waɗanda ake zargi da haddasa rikici a jam’iyyar APC.

Sanarwar ta yi zargin cewa an samu hare-hare kan tarukan jam’iyyun adawa, lalata kayayyakin kamfen da kuma cin zarafin magoya bayansu a jihohin Edo, Cross River, Gombe, Legas, Kebbi da Kaduna.

Kwamitin ya kuma tambayi dalilin da ya sa shugaban ƙasar bai yi magana kan wasu gwamnonin APC da ake zargi da yin barazanar kai hari ga magoya bayan jam’iyyun adawa ba.

Ta jaddada cewa ADC na da niyyar gudanar da kamfen cikin lumana, wanda zai mayar da hankali kan matsalolin da suka addabi ƙasar, ciki har da yunwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da cin hanci da rashawa.

Bugu da ƙari, ADC-PCC ta zargi APC da amfani da tashin hankali saboda, a cewarta, ba ta da ingantattun hanyoyin magance matsalolin da al’umma ke fuskanta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments