Saturday, November 14, 2026
HomeLabaraiLabaraiWata kungiya ta bukaci DSS ta binciki mutuwar Sheikh Yahaya Masussuka

Wata kungiya ta bukaci DSS ta binciki mutuwar Sheikh Yahaya Masussuka

Wata ƙungiya mai suna Sani Zangina Foundation for Humanity First ta yi kira ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ta gudanar da cikakken bincike kan mutuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.

Ƙungiyar ta gabatar da buƙatar ne cikin wata takardar ƙorafi mai kwanan watan 13 ga Nuwamba, 2026, wadda ta aika wa Darakta Janar na DSS a Abuja, inda ta buƙaci gano waɗanda ke da hannu a lamarin tare da tabbatar da adalci.

Shugaban ƙungiyar kuma wanda ya kafa ta, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya bayyana cewa marigayin ɗan asalin Jihar Bauchi ne, wanda ke zaune a Ƙaramar Hukumar Dutsinma ta Jihar Katsina.

Ya ce malamin ya shahara wajen wa’azin zaman lafiya, haɗin kai da mutunta ‘yancin addini.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments