Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa mafi yawan mabiya addinin Kirista da jam’iyyar ta tuntuba sun nuna amincewarsu da tikitin takarar Muslim-Muslim na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima.
Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, inda ya yi watsi da ra’ayin cewa tsarin tikitin na iya hana mabiya addinin Kirista samun wakilci ko jin muryoyinsu a gwamnati.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban APC ya bayyana matsayar tasa ne yayin da yake magana kan muhawarar da ake yi game da tsarin tikitin takarar da shugaban ƙasa da mataimakinsa dukkaninsu Musulmai ne.