Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da tarbar da aka yi masa a jihohin Akwa Ibom da Rivers, yayin ziyarar da ya kai yankin tare da Mataimakinsa, Kashim Shettima, da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu.
Tinubu ya bayyana hakan ne a saƙon da ya wallafa bayan ziyarar ta kwanaki biyu, inda ya ce daga Uyo zuwa Fatakwal, sun samu kyakkyawar tarba da nuna ƙauna daga al’ummar yankin.
A Akwa Ibom, shugaban ya yaba da ayyukan raya ƙasa da Gwamna Umo Eno ya gudanar, musamman a fannonin hanyoyi, sufurin jiragen sama da yawon buɗe ido. Ya kuma ce tashar Ibom Deep Sea Port na da babbar dama wajen bunƙasa kasuwanci da samar da ayyukan yi.
A jihar Rivers kuwa, Tinubu ya ce ya samu gagarumar tarba a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, inda ya yi magana kan ci gaban da aka samu, ƙalubalen da ake fuskanta da kuma damar da ake ƙoƙarin samarwa matasa.
Ya bayyana cewa zaɓen 2027 ya shafi makomar matasan Najeriya da irin ƙasar da ake ginawa domin su. Tinubu ya kuma gode wa Mataimakinsa, gwamnonin jihohin biyu, shugabannin jam’iyya, sarakunan gargajiya da al’ummar yankin bisa goyon baya da tarbar da suka yi masa.