Saturday, November 14, 2026
HomeLabaraiMutane 62 da suka yi mu’amala da mai cutar Ebola sun kammala...

Mutane 62 da suka yi mu’amala da mai cutar Ebola sun kammala zaman sa ido ba tare da an ga cutar ba — NCDC

Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce mutane 62 da suka yi mu’amala da matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo sun kammala kwanaki 21 na sa ido ba tare da samun sabuwar kamuwa da cutar ba.

Babban Daraktan hukumar, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a, inda ya ce mutum na ƙarshe ya kammala wa’adin sa ido.

Ya ce mutane 13 sun nuna alamun zazzabi ko wasu matsaloli, amma gwaje-gwaje sun tabbatar da cewa ba su kamu da cutar ba.

Haka kuma, an binciki wasu rahotannin mutane bakwai da ake zargin sun kamu da cutar a Adamawa, Rivers, Borno, Legas da Ekiti, amma duk sun gwada ba su da cutar.

Sai dai Idris ya yi gargaɗin cewa kammala sa ido ba yana nufin Najeriya ta ayyana kanta a matsayin ƙasar da ba ta da Ebola ba, don haka za a ci gaba da sa ido.

Ya ce an tabbatar da cutar a jikin matar a ranar 20 ga Oktoba a Abuja, bayan jami’an lafiya sun kai rahoton zargin kamuwa da cutar.

An kuma ƙarfafa matakan kariya a asibitoci, gano waɗanda suka yi mu’amala da ita da kuma samar da kayan kariya ga ma’aikatan lafiya.

Idris ya ce an dauki matar zuwa Switzerland a ranar 26 ga Oktoba domin ci gaba da kula da lafiyarta, inda daga baya ta warke, ta gwada ba ta da cutar kuma aka sallame ta.

A nasa martanin, Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce an fara kashi na biyu na ƙidayar kwanaki 42 da ake buƙata kafin a tabbatar da kawo ƙarshen yaɗuwar cutar a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments