Zainab Musa Kwankwaso, matar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta shigar da ƙarar neman a raba aurensu a wata kotu da ke Gudu, Abuja.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa takardun kotu sun nuna cewa Zainab, wadda ’yar tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce, ta nemi a raba auren bisa tsarin Khul’i, wanda mace ke neman saki a Musulunci ta hanyar mayar da sadakin da mijinta ya biya.
A cewar takardar sammacin kotun mai lamba CV/97/26, an umarci gwamnan da ya gurfana a gaban kotun ranar 17 ga Nuwamba, 2026.
Zainab da Abba Kabir Yusuf sun yi aure ne a ranar 29 ga Yuli, 2006, lokacin da Zainab ke aiki a matsayin hadimar mahaifinta. Ma’auratan sun haifi ‘ya’ya shida tare.
A cikin bayanan ƙarar, Zainab ta bayyana cewa zaman aurensu ya shiga mawuyacin hali sakamakon abin da ta bayyana a matsayin rashin kulawa, soyayya da kusanci tsakanin ma’auratan.
Ta kuma bayyana cewa ba ta da son ci gaba da zaman auren, tana mai cewa halin da ake ciki na iya sanya ta kasa sauke nauyin da Musulunci ya ɗora mata a matsayin mata.
Haka kuma, ta yi zargin cewa duk ƙoƙarin da aka yi na sasanta tsakaninsu da dawo da zaman lafiya bai haifar da nasara ba.
Saboda haka, ta bayyana shirinta na mayar da sadakin da gwamnan ya biya a lokacin aurensu domin samun damar raba auren bisa tsarin Khul’i.
Rahoton ya kuma danganta rikicin auren da saɓanin siyasa da ya shiga tsakanin gwamnan da tsohon ubangidansa na siyasa, wanda kuma shi ne mahaifin Zainab, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kimanin shekara guda da ta gabata.
A cewar majiyoyin jaridar, Zainab ta bar gidan gwamnatin Kano ranar 28 ga Oktoba zuwa gidan mahaifinta da ke Miller Road, Kano, kafin daga bisani ta tafi Abuja.
Rahoton ya kuma yi zargin cewa lamarin ya jawo kamen wasu jami’an tsaro da ke aikin gadin gidan gwamnatin da kuma gidan Kwankwaso, kafin daga bisani aka sake su bayan yi musu tambayoyi.
Haka kuma, an bayyana cewa ‘yan sanda sun gayyaci wasu daga cikin ‘yan uwanta domin yi musu tambayoyi kan zargin taimaka mata wajen barin Kano.