Kwamitin yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da ƙarfafa rikicin siyasa da kai hare-hare kan jam’iyyun adawa a sassan Nijeriya.
ADC-PCC ta bayyana hakan ne a martanin da ta mayar kan wata sanarwar Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC, wadda ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa ’yan adawa yayin tarukan siyasa.
Ta bayyana sanarwar APC a matsayin abin munafunci da karkatar da hankalin jama’a daga matsalar da ake ciki.
A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ADC-PCC, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, kwamitin ya bukaci APC ta ɗauki alhakin ayyukan mambobinta tare da kiran su da su daina abin da ta kira ƙara ta’azzara rikicin siyasa a ƙasar.
ADC-PCC ta yi zargin cewa APC da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da hannu wajen samar da yanayin tashin hankali da ke barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Ta kuma zargi ’yan bangar siyasar APC da tarwatsa tarukan adawa, kai wa magoya bayansu hari da lalata kayan yaƙin neman zaɓe a jihohi daban-daban.
Kwamitin ya kuma zargi wasu gwamnonin APC da hana jam’iyyun adawa amfani da wuraren taro, rusa ofisoshinsu, kai wa mambobinsu hare-hare da kuma lalata motocinsu.
Haka kuma, ta ce ana ƙuntata wa jam’iyyun adawa wajen rataya fastoci, sanya allunan tallan ’yan takara da gudanar da tarukan siyasa ta hanyar sanya musu kuɗaɗen da ta bayyana a matsayin masu tsada.
ADC-PCC ta danganta tarwatsa taron tattaunawa da jam’iyyar NDC ta shirya gudanarwa a Legas ranar Alhamis da abin da ta kira dabarun APC na tsoratarwa da hana ’yan adawa gudanar da harkokinsu.
Ta ce yayin da ’yan adawa ke tattauna matsalolin yunwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da cin hanci da rashawa, APC ta koma amfani da tashin hankali a matsayin dabarar yaƙin neman zaɓe.
Haka kuma, kwamitin ya ce yana tattara bayanan hare-haren da take zargin an kai wa mambobinta, kuma za ta miƙa rahotanni ga hukumomin shari’a da kare haƙƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa.
ADC-PCC ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya bi shawarar Farfesa Jerry Gana, tare da tabbatar da cewa harkokin siyasa a ƙasar na gudana cikin zaman lafiya da mutunta ’yancin dimokuraɗiyya.
Duk da zarge-zargen, kwamitin ya jaddada cewa ADC za ta ci gaba da gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana da mayar da hankali kan manufofi, tana mai cewa ba za ta bari tsoratarwa ko tashin hankali ya hana ta shirye-shiryen zaɓen 2027 ba.