Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutum huɗu bisa zargin kai hari wata gonar kiwon kaji da ke kan titin Yankaba, ta hanyar Tokarawa, tare da satar kayayyaki.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.
Ya ce waɗanda ake zargin sun kai harin ne a ranar 3 ga Nuwamba, 2026, inda suka yanka kaji 84 tare da satar kwandunan ƙwai 13 da wasu kayayyaki.
A cewar sanarwar, jami’an rundunar ta musamman ta SIS sun fara kama mutum biyu, kafin binciken da suka gudanar ya kai ga kama wasu mutum biyu.
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai buhunan abincin kaji 35, mota kirar Sharon Galaxy, wuka guda ɗaya da wuƙaƙen faɗa uku da ake zargin suna da tabon jini.
Rundunar ta ce an mayar da kayayyakin ga mai su, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargi.
Ta kuma bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda aka kama a kotu bayan kammala bincike.