Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargaɗin cewa bai kamata a dawo da tallafin man fetur a Najeriya ba tare da fara magance matsalar cin hanci da rashawa ba.
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na PAPShow, inda yake mayar da martani kan alƙawarin da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi na cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
Malamin ya ce duk da cewa ƙasashe da dama suna bayar da tallafi domin rage wa al’umma tsadar muhimman kayayyaki da ayyuka, Najeriya na buƙatar magance matsalar cin hanci da rashawa domin tabbatar da cewa ba a karkatar da kuɗaɗen gwamnati ba.
Ya ce sake buɗe tsarin tallafin man fetur ba tare da magance matsalar cin hanci da rashawa ba, na iya samar da wata dama ta karkatar da kuɗaɗen gwamnati.
Sai dai Sheikh Gumi ya jaddada cewa cire tallafin man fetur ba tare da samar da isasshen tallafi ga talakawa da masu ƙaramin ƙarfi ba, yana ƙara jefa su cikin matsin rayuwa.
Ya buƙaci gwamnati da ta ƙara yawan kuɗaɗen da take warewa domin shirye-shiryen jin ƙai da tallafa wa al’umma, musamman waɗanda ke cikin mawuyacin hali.