Friday, November 13, 2026
HomeKasuwanciDangote na shirin kara jarinsa a Afirka zuwa Dala biliyan 70 nan...

Dangote na shirin kara jarinsa a Afirka zuwa Dala biliyan 70 nan da 2030

Attajirin ɗan kasuwa, Aliko Dangote, ya bayyana shirin ƙara jarin kamfaninsa a faɗin Afirka daga Dala biliyan 50 zuwa dala biliyan 70 nan da shekarar 2030, domin faɗaɗa harkokin kasuwancinsa a nahiyar.

Dangote ya kuma bayyana shirin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 10,000 a faɗin Afirka, ciki har da Nijeriya, domin tallafa wa masana’antu da bunƙasa tattalin arzikin nahiyar.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da wasu masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta da ’yan jarida daga Arewacin Nijeriya, waɗanda suka ziyarci matatar man Dangote da masana’antar takin zamani da ke Legas a ranar Alhamis.

Attajirin ya ce rashin wadatacciyar wutar lantarki na daga cikin manyan ƙalubalen da ke hana ƙananan masana’antu da matsakaitan ’yan kasuwa samun ci gaba, musamman saboda tsadar amfani da janareto mai amfani da fetur da dizal.

Ya bayyana cewa a halin yanzu kamfaninsa na samar da kusan megawatt 1,500 na wutar lantarki domin gudanar da ayyukansa.

Sai dai ya ce ana sa ran ƙarfin zai kai tsakanin megawatt 4,500 zuwa 5,000 bayan kammala shirin Vision 2030.

Dangote ya jaddada cewa samar da ayyukan yi da bunƙasa masana’antu na daga cikin hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro. Ya kuma ce gwamnati na da alhakin samar da manufofi da yanayi mai kyau da za su ƙarfafa ’yan kasuwa su zuba jari.

Haka kuma, ya bukaci Nijeriya ta rage dogaro da fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafa su ba, yana mai cewa ya kamata a riƙa sarrafa kayayyakin cikin gida kafin fitar da su zuwa ƙasashen waje.

A cewarsa, noma da ma’adanai na daga cikin manyan fannoni da Arewacin Nijeriya zai iya cin gajiyarsu idan aka samar da isassun ababen more rayuwa da masana’antun sarrafa albarkatun ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments