Wednesday, November 11, 2026
HomeLabaraiManchester United ka iya sallamar kocinta, Michael Carrick

Manchester United ka iya sallamar kocinta, Michael Carrick

Rahotanni sun nuna cewa Manchester United na nazarin yiwuwar sallamar kocinta, Michael Carrick, sakamakon rashin kyakkyawan sakamakon da ƙungiyar ke samu a gasar Firimiya ta Ingila.

Rahotanni sun nuna cewa Manchester United na nazarin yiwuwar sallamar kocinta, Michael Carrick, sakamakon rashin kyakkyawan sakamakon da ƙungiyar ke samu a gasar Firimiya ta Ingila.

Ƙungiyar ta ci gaba da ba shi damar jagorantarta bayan ta sha kashi da ci 3-0 a hannun Bournemouth ranar 25 ga Oktoba. Sai dai canjaras 4-4 da ta yi da Aston Villa ranar Lahadi ya ƙara masa matsin lamba.

A halin yanzu, Manchester United tana matsayi na 18 a teburin gasar, bayan samun nasara a wasa ɗaya kacal cikin wasanninta 10 na Firimiya. A wasanni uku da Carrick ya jagoranta, ta yi nasara sau ɗaya, ta yi canjaras sau biyu.

Duk da cewa har yanzu ba a yanke hukuncin sallamarsa ba, mahukuntan kulob ɗin na duba waɗanda za su iya maye gurbinsa, ciki har da Eddie Howe, Julian Nagelsmann, Antonio Conte da Mauricio Pochettino.

Raunin da wasu ’yan wasa suka samu, matsalolin tsaro da kuma ɓarar da damarmakin cin ƙwallo na daga cikin ƙalubalen da ke fuskantar Carrick. Haka kuma, wasu ’yan wasan ƙungiyar sun nuna rashin gamsuwa da dabarun da yake amfani da su.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments