Thursday, November 12, 2026
HomeLabaraiZuwan tawagar APC jihar Edo ya kawo tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa...

Zuwan tawagar APC jihar Edo ya kawo tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa a Benin

Zuwan tawagar kamfen ɗin jam’iyyar APC mai goyon bayan shugaban ƙasa a birnin Benin, babban birnin jihar Edo, ya haddasa cunkoson ababen hawa a sassa daban-daban na birnin.

Zuwan tawagar kamfen ɗin jam’iyyar APC mai goyon bayan shugaban ƙasa a birnin Benin, babban birnin jihar Edo, ya haddasa cunkoson ababen hawa a sassa daban-daban na birnin.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya jagoranci tawagar, inda ya isa filin jirgin saman Benin da misalin ƙarfe 12 na rana tare da gwamnoni, ministoci, sanatoci da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu cunkoso mai tsanani a manyan hanyoyin birnin sakamakon toshe wasu hanyoyi da ke kaiwa fadar Oba da kuma filin wasa na Samuel Ogbemudia, inda aka shirya gudanar da gangamin siyasar.

Hanyoyin da abin ya shafa sun haɗa da Airport Road, Plymouth Road, Reservation Road, Exotic Road da Ekenwan Road, lamarin da ya tilasta wa wasu matafiya yin tafiya a ƙafa domin isa inda za su.

Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da hukumar kiyaye haɗurra ta FRSC sun bazama kan tituna domin daidaita zirga-zirga. Haka kuma, an rufe wasu ofisoshi a faɗin jihar domin bai wa ma’aikata damar tarbar tawagar APC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments