Wednesday, November 11, 2026
HomeLabaraiMagoya bayan ADC sun yi zanga-zanga kan hukuncin da ya soke yan...

Magoya bayan ADC sun yi zanga-zanga kan hukuncin da ya soke yan takararta

Magoya bayan jam’iyyar ADC sun gudanar da zanga-zanga a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, domin neman a ba su kwafin hukuncin kotun da ya soke shugabancin jam’iyyar tare da rushe takararta a zaɓen 2027.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa masu zanga-zangar sun haɗa da ’yan takarar ADC a mukaman siyasa daban-daban, waɗanda suka gudanar da zanga-zangar a ranar Laraba ƙarƙashin ƙungiyar Forum of ADC Candidates.

Masu zanga-zangar sun buƙaci kotun da ta gaggauta ba su kwafin hukuncin domin su samu damar yin amfani da shi wajen ɗaukaka ƙara.

Sun bayyana cewa samun kwafin hukuncin na da muhimmanci wajen ba su damar ci gaba da matakan shari’a kan hukuncin da ya shafi shugabancin jam’iyyar da takararta a zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments