Friday, November 13, 2026
HomeWasanniCristiano Ronaldo zai fara fitowa a shirin fim kan kwallon kafa

Cristiano Ronaldo zai fara fitowa a shirin fim kan kwallon kafa

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo, zai fara fitowa a wani sabon shirin fim mai dogon zango da ya shafi ƙwallon ƙafa, inda zai taka rawa a matsayin jarumi duk da cewa har yanzu yana ci gaba da buga ƙwallo a ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya.

Ronaldo ne dai ya bayyana hakan ta shafinsa na Instagram, inda ya sanar da cewa an riga an fara aikin ɗaukar shirin fim ɗin tare da wallafa wasu hotunan bayan-fage na yadda ake gudanar da aikin.

A cikin hotunan da ya wallafa, an ga wani ɓangare na filin wasan ƙungiyar Brentford ta Ingila, lamarin da ke nuna cewa ana gudanar da wani ɓangare na ɗaukar shirin a filin wasa na gaske a Ingila.

Wannan sabon aikin na nuni da wani sabon fanni da Ronaldo zai shiga a wajen harkar ƙwallon ƙafa, yayin da yake ci gaba da taka leda a matakin ƙwararru.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments